A Kamaru, labarin dakatar da wadanan kungiyoyi ya tayar da hankulan kungiyoyin kare hakokin bil Adam na ciki da wajen kasar.
An dakatar da kungiyoyi masu zaman kansu guda uku na tsawon watanni uku, sannan hukumomin suka kuma sanar da dakatar da wasu biyu.
Wasu kungiyoyi biyu na Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam a Afirka ta Tsakiya (Redhac), kungiyar agaji ta al'adu ta Kamaru da kuma kungiyar Reach Out Kamaru da ke Bueya, a kudu maso yammacin kasar na daga cikin wandada dokar ta shafa.
Paul Atanga Nji, ministan kula da yankuna na Kamaru, ya bayar da hujjar dakatar da wasu kungiyoyi masu zaman kansu guda uku da kuma haramtawa wasu biyu ci gaba da gudanar da ayukan su a kasar.
Ya ba da misali da zarge-zargen da ake yi wa wadanan kungiyoyi na amfani da kuɗaɗen da nufin tallafawa ayukan ta’addanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI