Shugaban hukumar zaben Isie, Farouk Bouasker, ya yi la'akari da kashi 27.7% na mutane ne suka fito a zaben na yau Lahadi, duk da cewa shi ne mafi karancin adadi a zaben kasar Tunisia musaman zaben shugaban kasa zagaye na farko tun bayan zuwan dimokuradiyya a 2011 a wannan kasa.
Magoya bayan Shugaba Kaïs Saïed AP - Anis MiliShugaban kasar mai barin gado Kais Saied shi ne ya lashe sama da kashi 89% na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar da aka gudanar a yau Lahadi , kamar yada wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da gidan talabijin na kasar Wataniya ya watsa.
Saied, mai shekaru 66, ya fi rinjaye, bisa ga wannan kuri'ar da cibiyar Sigma Conseil ta gudanar, dan masana'antu mai sassaucin ra'ayi Ayachi Zammel, wanda ya samu kashi 6.9% na kuri'un da aka kada, da kuma tsohon mataimakin kungiyar kasashen Larabawa, Zouhair Maghzaoui. , na karshe da kashi 3.9% na kuri'un.
Daya dag cikin magoya bayan Shugaban Tunisia © FETHI BELAID / AFPYan takara da bangaren adawa da suka samu tikitin shiga zaben sun hada da Zouhair Maghzaoui, mai shekaru 59, wanda tsohon mamba ne na kungiyar kasashen Larabawa ta hagu, da kuma Ayachi Zammel, mai shekaru 47, wani masanin masana'antu masu sassaucin ra'ayi da jama'a ba su sani ba, wanda ya kasa yin yakin neman zabe saboda an daure shi a gidan yari.
Tun daga shekarar 2021, kungiyoyi masu zaman kansu na Tunisia da na kasashen waje da kuma 'yan adawa, wadanda aka kama manyan jiga-jigan su, sun yi Allah wadai da rawar mulkin Kais Saied.
Shugaban Tunisia da matarsa © Anis Mili / APA cewar Human Rights Watch, "fiye da mutane 170 a halin yanzu ana tsare da su saboda dalilai na siyasa ko da kuma tauye musu hakkokinsu."
Shugaba Saied har yanzu na samun "gagarumin goyon baya a tsakanin ma'aikata"duk da cewa y ana fuskantar suka saboda gazawar da ya yi wajen fitar da kasar daga cikin mawuyacin hali na tattalin arziki".
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI