Kabila da Katumbi sun haɗa kai wajen zargin shugaba Tshisekidi da kama karya

Kabila da Katumbi sun haɗa kai wajen zargin shugaba Tshisekidi da kama karya

Sama da shekaru biyu kenan tun bayan ganawarsu ta ƙarshe a Lubumbashi, lokacin wani taron hadin kan kansa, mutanen biyu, wadanda a baya abokan hamayya ne sun soki gwamnatin Tshisekedi da ta'azzara matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.

Sanarwar ta nuna rashin jin dadin yadda matsalar tsaro ke ƙara ta'azzara, inda ƴan tawayen M23 suka kwace yankuna da dama a gabashin kasar.

Sun yi kira ga ƴan siyasa da su hada kai don yakar abin da suka bayyana a matsayin mulkin kama karya.

Saidai Kinshasa na, zargin mutanen biyu da hada kai da Rwanda, wadda Majalisar Dinkin Duniya ke zarginta da goyon bayan ƴan tawayen M23 da ke kai farmaki a DRC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)