Sojojin Burkina Faso da ke da sansani a Sebba, a arewa maso gabashin ƙasar , sun fuskanci wani mummunan hari da rahotanni suka tabbatar da cewa ya kashe aƙalla sojoji 29 da fararen hula 7, cika har da wata mata da yaranta 4.
Yayin da ya zuwa yanzu gwamnatin sojin ƙasar ba ta ce komai ba kan harin, ƙungiyar JNIM da ke samun goyon bayan al-Qaeda, ta ɗauki alhakin kai harin, tare da sanar da kwace iko da sansanin sojin na Sebba.
Haka zalika, mayakan sun banka wuta a cibiyar makamashin gas ɗaya tilo da ake da ita a Sebba, da kuma cibiyar kula da lafiya ta yankin mai aikin tiyata.
Kamar makwaftanta da suka haɗa da Mali da Jamhuriyar Nijar, Burkina Faso na fama da tashe-tashen hankula tun shekarar 2015, sakamakon ƙungiyoyin mayaka masu iƙirarin jihadi, waɗanda suka yi wa ƙungiyar Al-Qaeda da IS mubaya’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI