Jirgin ruwa ya kife a Laberiya

Jirgin ruwa ya kife a Laberiya

Mutane 11 sun rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin ruwa dauke da fasinjoji a Monrovia Babban Birnin Laberiya.

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun rawaito Kwamishinan Hukumar Kula da Sufurin Teku na Laberiya Eugene Lenn Nagbe na cewa, jirgin ruwan da ya tashi daga Monrovia zuwa Buchanan ya kife.

Nagbe ya ce, a aiyukan ceton da aka gudanar bayan afkuwar ibtila'in an ciro jikkunan mutane 11.

Nagbe ya kara da cewa, a kalla mutane 15 sun bata, kuma ana ci gaba da aiyukan neman su.

Sakamakon ruwan sama koguna na cika a Laberiya wanda hakan ke janyo hatsarin jiragen ruwa.

 


News Source:   ()