Mutum 1 ya rasa ransa, an nemi wasu 24 an rasa sakamakon kifewar jirgin ruwan kwale-kwale a kasar Gana.
Hukumar Yaki da Magance Annoba (NADMO) ta bayyana cewar sakamakon loda kaya da suka wuce ka'ida aka yi wa wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji da ya tashi daga garin Agalarkope zuwa kauyen Dzemeni ne aka samu hatsari a kogin Volta.
Sanarwar ta ce a aiyukan bincike da aka gudanar an samu gawar mutum 1, yayinda ake ci gaba da neman wasu mutanen 24 da suka bata.