Jirgin da ya toshe mashigar Suez ya haifar da hasarar miliyoyin dala a Masar

Jirgin da ya toshe mashigar Suez ya haifar da hasarar miliyoyin dala a Masar

A Masar an yi watsi da rokon da aka yi game da shawarar tsare jirgin "The Ever Given", wanda ya sa aka rufe hanyar Suez ta kwanaki.

A cewar rahotanni na kafofin watsa labarun cikin gida, Kotun Tattalin Arziki ta Ismailiyye ta yanke hukunci kin amincewa da bukatar tsare jirgin.

Kotun ta sake tura karar zuwa Ismailiyye Kotun Tattalin Arziki ta Farko don tantancewa a ranar 29 ga Mayu.

Ahmed Ebu Sheneb, wanda ke cikin kwamitin tsaro na kamfanin da ya mallaki jirgin, ya bayyana cewa kin amincewar da kotun ta yi wa rokon ya nuna cewa za'a ajiye jirgin a yankin Lakes na Suez Canal.

Babbar jirgin kwantenar mai suna "The Ever Given" ya faɗa cikin mashigin Suez a ranar 24 ga Maris, sakamakon rashin gani sosai saboda guguwar kasa da kuma yanayi mara kyau.

hakan ya haifar a rufe hanya lamarin da ya sanya matsalar rashin shiga ta fitar kayayyakin gas da danyen mai a yankin na kwanaki.

Hukumar kula da mashigar ruwa ta Suez ta sanar da cewa a kokarin da aka yi  a ranar 29 ga Maris, bayan kwanaki 6 na aiki, an kammala shi cikin nasara kuma an bude mashigar don zirga-zirgar jiragen ruwa.

A wannan tsarin, an kiyasta cewa Masar ta yi asarar kusan dala miliyan 12-14 a kowace rana, yayin da The Ever Given, wanda ya koma yankin tabkuna bayan hatsarin, ya ba da asarar kusan dala biliyan 10 a kasuwancin duniya.


News Source:   ()