Jiragen ruwan masunta 2 dauke da mutane 17 sun kife a kogin Maryut da ke Masar.
Rahotannin farko da aka samu sun bayyana mutuwar mutane 7.
Sanarwar da helkwatar 'yan sandan Iskandariyya ta fitar ta ce, jiragen ruwan 2 dauke da mutane 17 daga iyali daya sun kife a kogin Maryut, kuma ya zuwa yanzu an tsamo jikkunan mutane 7.
An aike da jami'an tsaron teku, motocin daukar marasa lafiya da ma'aikatan ceto zuwa yankin.
Jiragen ruwan 2 sun kife bayan dawowa daga cin abincin dare a wani tsibiri da ke da kauyawa a cikinsa.
Ana ci gaba da neman mutane a kogin.