Wasu daga cikin jihohin da ke fuskantar haɗarin aukuwar ambaliyar ruwan saboda fara buɗe dam ɗin Lagdon akwai Benue, Nasarawa, Kogi, Bayelsa, Delta da kuma Rivers, inda ƙwararru suka buƙaci hukumomi a matakin tarayya da na jihohin su sa ido da kuma tsaurara matakan rigakafi don rage tasirin iftila’in ambaliyar da ake hasashe.
Wannan gargadi ya zo ne a dai dai lokacin da ake cigaba da ayyukan agaji a jihar Borno, inda ambaliyar ruwa ta raba miliyoyin mutane da muhallansu a garin Maiduguri, bayan ɓallewar da bakin dam ɗin Alau saboda tumbatsar da yayi, sakamakon saukar ruwan sama babu ƙaƙƙautawa, wanda baya ga Najeriya ya haddasa ambaliya a Kamaru, da Chadi, da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar, sassan da a baya basu saba samun saukar isasshen ruwan ba.
A shekarar 2022, mutane fiye da 600 suka rasa rayukansu a Najeriya, yayin da kuma aka tafka hasarar ɗaruruwan gonaki, sakamakon ambaliyar da ta biyo bayan saukar ruwan sama kamar da bakin ƙarya da kuma sakin ruwan dam ɗin Lagdo na Kamaru, lamarin da masana suka ce za a iya kauce masa ko kuma takaita tasirinsa, inda mahukuntan Najeriya sun gina madatsun ruwan da za su riƙa ɗauke ruwan katafaren dam ɗin da ke kwararowa daga makwaftan nasu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI