Janaral Mahamat Deby ya maye gurbin mahaifinsa da aka kashe a filin daga

Janaral Mahamat Deby ya maye gurbin mahaifinsa da aka kashe a filin daga

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby Itno ya rasa ransa sakamakon raunin da ya samu a lokacin da suke fafata rikici da 'yan tawaye, kuma tuni rundunar sojin kasar ta sanar da dansa Janaral Mahamat Kaka Deby a matsayin wanda zai shugabanci kasar.

A ranar 11 ga watan Afrilu aka gudanar da zaben Shugaban Kasa a Chadi kuma Deby ya samu kaso 79,32 inda ya sake samun nasara bayan shugabantar Chadi na tsawon shekaru 30.

A makon da ya gabata ne aka fara rikici tsakanin Larabawa, kabilun Dagal da Kibet da ke kauyukan Sihep da Ambarit na yankin Salamat din kudancin Chadi inda ya zuwa yanzu aka kashe mutane sama da 100.

Gwamnan Salamat Janaral Yambaye Massyra Abdel a makon da ya gabata ya fadi cewa, an bude wuta kan gidaje da dama a yayin rikicin, kuma sun aika da jami'an tsaro don kama wadanda suka haddasa rikicin.


News Source:   ()