Janar Haftar na Libya ya gana da shugaban Faransa Macron a birnin Paris

Janar Haftar na Libya ya gana da shugaban Faransa Macron a birnin Paris

Bayanai sun ce shugabannin biyu, sun tattauna kan batutuwa da dama ciki har da shirin siyasar ƙasar Libya da kuma muhimmancin goyon bayan ayyukan dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya.

Libya ta dauki dogon lokaci tana neman shawo kan matsalolin da suka addabeta sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar da akayi a shekarar 2011, ƙarƙashin taimakon kungiyar NATO wajen hamɓarar da shugaban kasar Muammar Ghadafi, da kuma hallaka shi.

Tun a wancan lokaci kasar ta dare gida biyu, inda ta samu gwamnatoci biyu, daya a Tripoli, daya kuma a Benghazi.

Ƙasar Faransa ta bukaci hukumomin Libya da su saki Mahmoud Salah, wanda dakarun Haftar suka kama, saboda zargin shirin kuɓutar da tsohon shugaban Nijar Bazoum Mohammed.

Faransa ta bayyana adawar ta da shirin daukar Salah zuwa Nijar domin fuskantar tuhuma a hannun gwamnatin sojin kasar.

Rahotanni sun ce tatatunawar ta kuma ƙunshi yuwuwar kafa sansanin soji a Loig da ke kudancin Libya, kusa da iyakar Nijar.

Hotunan da aka rabawa manema labarai bayan ganawar, sun nuna yadda shugabanin biyu suka yi musabaha, yayin da shugaba Macron ya jaddada muhimmancin gudunmowar Haftar akan shirin siyasar Libya.

Yunƙurin sasanta rikicin Libya da kuma gudanar da zabe, na ci gaba da fuskantar koma baya, saboda yadda ɓangarorin dake kokawar neman ikon ƙasar, suka gaza haɗa kawunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)