Janar Assimi Goïta, "ya gayyaci gwamnati da ta fayyace hanyoyin shirya zabe a Mali

Janar Assimi Goïta, "ya gayyaci gwamnati da ta fayyace hanyoyin shirya zabe a Mali

Shugaban kasar, Janar Assimi Goïta, "ya gayyaci mambobin gwamnati da su samar da sharuddan da suka dace don shirya zabuka cikin gaskiya da lumana wanda ya kamata ya kawo karshen mika mulki", kamar dai yadda wani rahoto daga fadar Gwanatin kasar ya tabbatar.

Tun a shekara ta 2020 bayan karbar mulki,sojoji suka bayyana aniyar su da cewa suna son daidaita kasar Mali, dake fama da tashin hankali da rashin tsaro a wasu yankuna musamman a arewacin kasar.

Tsohon Firaminista Choguel Maïga da Shugaban Majalisar sojin kasar Mali Assimi Goïta Mali Tsohon Firaminista Choguel Maïga da Shugaban Majalisar sojin kasar Mali Assimi Goïta Mali © Michele Cattani AFP - Ousmane Makaveli AFP

Sanarwar Janar Assimi Goita na zuwa kusan makonni biyu da cire Firaminista Choguel Maiga,wanda ya bayyana damuwar sa da abinda ya kira shuru daga hukumomin sojin Mali a kan batun da ya shafi mika mulki  da shirya zabe a wannan kasa ta Mali.

Da farko dai sojoji sun yi alkawarin ba da dama ga farar hula a watan Maris na 2024 bayan zaben shugaban kasa. Sun koma kan wannan alkawari ba tare da sanya wani sabon wa'adi ba. Ana daukar Janar Goïta a matsayin wanda zai iya tsayawa takarar zaben shugaban kasa a nan gaba. Tun daga shekara ta 2020, sojojin sun kara nisanta kan su daga Faransa,tare da karfafa huldar ta da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)