Sakatare Janar na jam’iyyar RDPC da ke mulkin ƙasar shekaru da dama Jean Nkuete ne ya nuna bacin ransa cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce wasu ƴan kasar ciki harda ƴan adawa da malaman addinin na wuce gona da iri wajen furta wasu kalamai na cin mutunci da kushe gwamnatin shugaba Paul Biya, shugaban jam’iyyar kuma ɗan takara a zaɓen dake tafe.
Babban mai kula da jam’iyyar dake mulki sama da shekaru 60, na martani ne sakamakon cece-kece da ya ɓarke a ƙasar da ke tsakiyar Afirka tun ranar 31 ga watan Disamba, lokacin da wasu fada-fadar mujami’ar Katolika a jihohin ƙasar daban-daban suka sanar da dawowa daga rakiyar takarar shugaba Paul Biya da ya kwashe sama da shekaru 40 yana mulki, a sakonninsu na ƙarshen shekara.
Jean Nkuete ya ce kiranye kiranyen da Fada-Fadar masamman na Douala da Yaounde da Yagoua da Ngaudere ke yi na Paul Biya ya je ya huta, babu abin da zai haifar face haddasa fargabata da ruɗani tsakanin ƴan ƙasar, yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa a watan Oktoba mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI