Jam'iyyar Pastef ta Diomaye Faye ta lashe kashi uku cikin hudu na kujerun majalisa

Jam'iyyar Pastef ta Diomaye Faye ta lashe kashi uku cikin hudu na kujerun majalisa

Jam'iyyar Pastef ta shugaba Bassirou Diomaye Faye ta samu kujeru 130 a majalisar dokokin kasar mai kujeru 165.Sakamakon zaben na ranar Lahadi ya kasance na wucin gadi, har zuwa lokacin da majalisar tsarin mulkin kasar ta tabbatar a cikin kwanaki biyar.

Zai kasance mafi yawan rinjaye da jam'iyya daya ta taba lashe a zaben 'yan majalisa.

Tarihi ya nuna cewa Jam'iyyar gurguzu ta samu kujeru 103 daga cikin 120 karkashin shugaba Abdou Diouf a shekarar 1988, inda tun daga lokacin da aka samu rinjaye  kamar a shekarar 2012.

Magoya bayan shugaban kasar Senegal Magoya bayan shugaban kasar Senegal REUTERS - Zohra Bensemra

Gamayyar hadakar tsohon shugaban kasar Macky Sall ta samu 'yan majalisa 16 kacal, inda bakwai na tsohon firaministan kasar Amadou Ba, uku kuma na magajin garin Dakar Barthelemy Dias, kamar yadda sakamakon wucin gadi ya nuna. Firaminista Ousmane Sonko mai matukar tasiri kuma mai kwarjini, wanda shi ne dan takara na Pastef, ana daukarsa a matsayin wanda ya shirya zaftarewar majalisar.

Bayan da suka hau karagar mulki watanni takwas da suka gabata, dole ne sabbin shugabannin su tunkari abin da al'ummar Senegal masu fama da tashe-tashen hankula ke yi, bayan da suka yi alkawarin kawo sauyi mai zurfi a cikin tsarin da suka yiwa sunan sauyin tsarin da Senegal ta dace ko salon Pan-Africanism na hagu.

Magoya bayan jam'iyya mai mulki a Senegal Magoya bayan jam'iyya mai mulki a Senegal AFP - SEYLLOU

Manufar ita ce "sauyin tsarin da Senegal ta dace," in ji Shugaban kasar Faye a taron majalisar ministocin na ranar Laraba.

Shugaban kasar Faye ya yi magana game da bukatar tunkarar matsalolin gaggawa na tattalin arziki da zamantakewa kamar tsadar rayuwa da rashin aikin yi, tare da farfado da tattalin arziki, "musamman a bangaren noma, kiwo, yawon bude ido, hakar ma'adinai da ma'adinan ruwa". Alkaluman hukumar ta kasa, tarin sakamako ne da aka buga a matakin sassan ranar Talata, wanda tuni ya nuna nasarar Pastef.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)