jam'iyya mai mulkin Mozambique ta yi gagarumar nasara a zaɓen ƙasar

jam'iyya mai mulkin Mozambique ta yi gagarumar nasara a zaɓen ƙasar

Sakamakon zaben da aka fitar a jiya Alhamis ya nuna cewar Daniel Chapo, dan takarar jam’iyyar FRELIMO da ta shafe shekaru 50 tana mulkin Mozambique ne ya lashe zaben na shugaban kasa da kashi 71 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada.

Jagoran ‘yan adawa Venancio Mondlane da ayyana kansa matsayin wanda yayi nasarar gabanin fitar da sakamakon kuwa, kashi 20 na kuri’un da kada yayin zaben ya samu.

A zaben majalisar dokoki ma dai jam’iyya mai mulkin ta FRELIMO ce ta samu nasara da gagarumin rinjaye, inda ta lashe kujeru 195 daga 250, yayin da jami’iyyar Podemos ta jagoran ‘yan adawa Mondlane ta samu kujeru 31.

Bayanai sun ce tun kafin fara sanar da sakamakon zaben a jiya, dubun dubatar magoya bayan Venancio Mondlane suka yi gangami a biranen Mozambique, ciki har da babban birnin kasar Maputo, basu kuma bata lokaci wajen fantsama kan titunana ba cikin fusata a daidai lokacin da hukumar zabe ke tsaka da sanar da sakamakon zaben, lamarin da ya haifar da arrangama tsakanin ‘yan adawar da jami’an tsaro, abin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda da jikkatar wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)