Jami'an tsaron Najeriya sun cafke bakin haure sama da 160

Jami'an tsaron Najeriya sun cafke bakin haure sama da 160

Cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai, kakakin ‘yan sandan a Kebbi Nafi’u Abubakar, ya ce daga cikin mutanen da suka cafke a Birnin Kebbi, 35 ‘yan Burkina Faso ne, 11 daga Jamhuriyar Benin, sai ‘yan Nijar 5 da kuma ‘yan ƙasar Mali 4, yayin da yawan ‘yan Ivory Coast ya kai 110.

Sanarwar ta ƙara da cewa, mutanen marasa takardun shiga da kuma yin aiki a Najeriyar, sun ƙare wajen aikata damfara.

Rundunar ta ce tuni aka miƙa baƙin hauren, zuwa ofishin hukumar shige da fice da ke jihar Kebbi, domin gudanar da cikakken bincike kafin ɗaukar matakin shari'a a kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)