A cewar ɗaya daga cikin lauyoyin Yves Kibouy Bershu- wanda aka fi sani da Steve Akam, amma kuma yake amfani da Ramon Cotta a shafukan sada zumunta, ƴan sandan sun basu damar ganawa ta sa'o'i 2 amma ba tare da an bayyana abin da ake tuhumar sa ba.
Emmanuel Chendjou, ɗaya daga cikin lauyoyinsa yace an kama matashin da ya yi fice wajen sukar shugabannin ƙasar a tsakiyar watan Yuli a makwabciyar ƙasar Gabon, inda ya ke zaune, kuma nan take suka tisa ƙeyarsa zuwa Kamaru, daga nan ne aka daina jin labarinsa.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, lauyoyin Ramon Cotta sun ce ya bayyana musu irin akuɓar da aka yi masa, kuma sun tabbatar da tabbunna a jikinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI