Jami'an tsaro sun kama mutane da dama a Sudan ta Kudu sakamakon zanga-zanga

Jami'an tsaro sun kama mutane da dama a Sudan ta Kudu sakamakon zanga-zanga

Zanga-Zangar ta barke ne a Juba babban birnin kasar a makon da ya gabata, sakamakon rahotannin da ke cewa rikicin da ya barke a makwabciyarta ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 29 ƴan ƙasar ta Sudan ta Kudu, rikicin da ya rikide zuwa tarzoma da ta bai wa bata gari damar fasa shaguna da kuntuka wa mutane sata.

Tarzomar ta bazu a cikin ƙasar  inda jami’an tsaro suka rinka harbin mutane don tarwatsa dandazon masu zanga-zangar, da ga bisani kuma suka kama mutane da dama wadanda ba a tabbatar da adadin su ba.

Kakakin rundunar ƴan sandan ƙasar John Kassara ya bayyana cewa  mutane 600 da aka kama, suna da hannu wajen fasa shaguna da tserewa daga wajen da sojoji ke tsare da su a Juba.

A kalla mutane 16 ne aka kashe a rikicin da ya ɓarke a makon da ya gabata, tare da raunata gommai, sannan wasu daruruwa suke neman mafaka a caji ofis.

Tuni dai gwamntin shugaba Salva Kiir ta sanya dokar hana fitar dare a yankin, don tabbatar da zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)