Jamhuriyar Kamaru ta yi wa mayakan Boko Haram kimanin 700 afuwa

Jamhuriyar Kamaru ta yi wa mayakan Boko Haram kimanin 700 afuwa

Wannan na zuwa ne, daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin masu dauke da makamai da 'yan tawaye, musamman daga yankin arewa mai nisa.

Rikicin mayakan Boko Haram ya haifar da matsalar jin kai, musamman a yankin Sahel, inda miliyoyin mutane suka tserewa muhallansu domin neman mafaka.

Ko a baya-bayan nan anyi artabau tsakanin mayakan da sojojin kasar Chadi, inda wani harin kwanton bauna da mayakan suka kai wani barikin soji ya kashe sojojin kasar sama da 40.

RFI ya gano cewa daga cikin wadanda aka yi wa afuwar akwai ‘yan Nigeria, Chadi da kuma kasar Kamaru.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Lourwanou Shehu Ousmanou, 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)