Zuwa yanzu cutar ta harbi mutane dubu 17,500 cikinsu kuma 629 sun rasa ransu tun daga lokacin da cutar ta fara mamaya a farkon shekarar da muke ciki.
Da yake jawabi ministan lafiya na ƙasar Samuel-Roger Kamba ya ce waɗanan allurai zasu taimaka ƙwarai wajen yaƙi da cutar da kuma samar da kariya ga waɗanda basu kamu ba.
Alluran da ƙasar ta karɓa, kason farko ne da cikin guda dubu 200 da ƙungiyar tarayyar turai ta alƙawarta mata.
A nasa bangaren shugaban hukumar lafiya ta ƙungiyar tarayyar turai Laurent Muschel ya ce kafin ranar 8 ga watan gobe ranar da jamhuriyar dimokradiyyar Congo zata fara gangamin gudanar da allurar rigakafin za’a cika mata saura.
Muschel ya ce ƙungiyar tarayyar turan ta ware jimillar alluran guda dubu 560 don rabawa ƙasashen nahiyar Afrika da aka sami ɓullar cutar.
Kamar yadda mai saurare ya sani ne, ƙasar itace cibiyar cutar, inda ta faro kafin daga bisani ta tsallaka zuwa sauran ƙasashe maƙwafta, sannan aka ji ɓullarta a wasu sassan turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI