Jamhuriyar Congo ta yanke hulda da Rwanda bisa zargin taimakawa 'yan tawaye

Jamhuriyar Congo ta yanke hulda da Rwanda bisa zargin taimakawa 'yan tawaye

Tuni kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani taron gaggawa a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin Congo da 'yan kungiyar M23 masu dauke da makamai.

Rikici tsakanin ‘yan tawayen M23 da aka kwashe shekaru uku ana yi a gabashin kasar mai arzikin ma'adinai ya tsananta a wannan watan, inda 'yan tawayen suka karbe iko da wasu yankuna, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin hadarin da ke tattare da yankin.

Dakarun Congo da dakarun wanzar da zaman lafiya na kokarin dakile ci gaban da kungiyar M23 ke samu, musamman a gabashin birnin Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa.

M23, kungiya ce mai dauke da makamai wacce ta balle daga sojojin Jamhuriyar Congo sama da shekaru 10 da suka gabata, kuma tun bayan bullarta a shekarar 2022, kungiyar ta ci gaba da samun nasara a gabashin kasar.

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Majalisar Dinkin Duniya na zargin Rwanda da tallafawa ‘yan tawayen na M23 da sojoji da makamai, abin da gwamnatin Rwanda ke ci gaba da musantawa.

Akalla dakarun wanzar da zaman lafiya tara, da suka hada da biyu daga rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD MONUSCO, aka kashe a fadan da ake yi a gabashin kasar.

Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na AP cewa, sojojin Majalisar biyu aka kasha a ranar Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)