Wannan matakin wata matsaya ce ta ƙasar ta Benin a gwamnatance dangane da hasashen da shugaban Nijar ya yi, wadda Benin ta bayyana a matsayin mara tushe.
Cikin sakon jawabin da ma’aikatar harkokin wajen Benin ta fitar a shafinta na X a ranar Talata da ta gabata, ministan ma’aikatar Olusegun Bakari ya shaida cewa tabbatas sun turawa jakadan Nijar sammaci domin ya ba da bahasi a game da zargin da ƙasarsa ta yi musu.
"Saboda zarge-zargen da ake yi wa kasarmu, an gayyaci jami'an tsaro na Nijar," in ji ma'aikatar harkokin wajen Benin a shafin ta na X, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Har ila yau, ma'aikatar ta aike da wasikar zanga-zangar, inda ta yi watsi da zarge-zargen tare da jaddada kudurin kasar na samar da zaman lafiya da hadin gwiwa da makwabtanta.
Rikicin na diflomasiyyar ya samo asali ne daga jawabin ranar Kirsimeti da Tchiani ya yi, inda ya zargi kasar Benin da zama cibiya ga 'yan ta'adda da ke neman tada zaune tsaye a Nijar.
Zargin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar kalubale a yankin tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar wanda ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin shekarar 2023.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI