Jamhuriyar Benin ta ci tarar wasu kamfanonin sadarwa 2 kuɗi Euro miliyan 7

Jamhuriyar Benin ta ci tarar wasu kamfanonin sadarwa 2 kuɗi Euro miliyan 7

Dama dai hukumar ta Arcep-Benin ta jima tana bibiyar kamfanonin 2 wato Spacetel and Moov Africa Benin wanda ta gano sun gaza wajen samar da yanayin sadarwa mai ƙarfin 3G zuwa 4G a wasu manyan titunan ƙasar 11, kamar yadda kamfanin dillancin labarai Faransa na AFP ya ruwaito.

Tun cikin watan Disimbar 2020 aka cimma yarjejeniyar kammala wanann aiki, amma kamfanonin suka gaza wajen aiwatar da shi, lamarin da tuni suka amince da gazawa, wanda ta sa hukumar cin tarar su kan kuɗi sama da CFA biliyan 3 kwatankwacin Euro miliyan 7.

Benin wadda ke da kamfanoni sadarwa 3 da suka yi fice a ƙasar da suka haɗa da Spacetel na Afrika ta Kudu da kuma na Marocco Moov Benin, sai kuma mallakinta Celtiis an kafa su ne a cikin shekarar 2022.

a halin yanzu dai an bai wa kamfanonin watanni 12 don ganin sun inganta ƙarfin sadarwarsu ko su fuskanci wani sabon hukunci mai tsauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)