Jama'ar yankin Jufra na Libiya sun gudanar da zanga-zangar la'antar Haftar

Jama'ar yankin Jufra na Libiya sun gudanar da zanga-zangar la'antar Haftar

Jama'ar garin Jufra na Libiya sun gudanar da zanga-zangar la'antar Haftar dan tawaye Haftar Khalifa sakamakon garkuwa da wani mutum tare da kashe shi da mabiyansa suka yi.

Jama'ar na yankin Hun sun taru tare da la'antar Haftar da mabiyansa bisa garkuwa da wani dan kasar Libiya, kuma suka kashe shi.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta sanar da tashar talabijin ta Febrayer cewa mayakan Haftar sun yi garkuwa da wani mutum mai suna Tarik Abdulhafiz inda bayan azabtar da shi na mako huda suka kashe shi.

Mazauna garin Hun sun harzuka bayan samun labarin kashe mutumin inda suka rufe dukkan hanyoyin da ke zuwa yankin tare da kai hari kan motocin mayakan Haftar.

A ranar 3 ga watan Yuli ma jama'ar Hun sun gudanar da zanga-zanga bayan da wani sojan haya dan Janjawid da aka kawo daga SUdan ya bude wuta tare da kashe wani mutum da ke tsaye a kofar gidansa. An kona wurare da dama da mayakan Haftar suke zaune.


News Source:   www.trt.net.tr