Jam'iyyar RHDP mai mulki a Ivory Coast ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar 6 ga Maris.
Sakamakon da Hukumar Zabe ta sanar ya bayyana cewa, jam'iyyar HRDP ta shugaba Alassane Ouattara ta samu rinjaye inda ta lashe kujeru 137 daga cikin 255 na majalisar dokoki.
Akwai kusan masu jefa kuri'a miliyan 7 a kasar, kuma kaso 37 ne kadai suka fita rumfunan zabe.
A watan Oktoban 2020 Ouattara ya lashe zaben Shugaban Kasa wanda hakan ya ba shi damar fara zango na 3 a mulkin kasar.