Jakadan Italiya a Kongo ya mutu sakamakon harin 'yan ta'adda

Jakadan Italiya a Kongo ya mutu sakamakon harin 'yan ta'adda

Jakadan Italiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Luca Attanasio tare da sojan Italiya 1 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kaiwa jerin gwanon motocin Majalisar Dinkin Duniya.

Rubutacciyar Sanarwar da aka fitar daga Ma'aikatar Harkokin Wajen Italiya ta ce,

"Muna matukar bakin ciki da samun labarin rasuwar jakadanmu Luca Attanasio a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo."

Sanarwar ta ce, harin da aka kai kan dakarun MDD a Kongo ya rutsa da Attanasio da wani Jandarman kasar 1.

Labaran da aka fitar a jaridun Italiya sun ce, an yi yunkurin garkuwa da mutanen da ke cikin jerin gwanon motocin a yayin kai harin.


News Source:   ()