A wata sanarwar da shugaban ƙasar Nangolo Mbumba ya fitar, ta ce tsohon shugaban jamiyyar SWAPO Sam Nujoma ya rasu ne a ranar asabar ɗin da ta gabata, bayan jinyar makonni 3 a wani asibitin da ke Namibia.
Marigayin ya shafe shekaru 30 yana yaƙin nemar wa ƙasar ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka, wanda ya kai ga cimma burinsa a shekara 1990, kuma ya zamo shugaban ƙasar na farko ƙarƙashin mulkin farar hula.
Tuni dai shugabannin ƙasashe suka fara tura saƙon ta’aziyyarsu ga gwamnati da al’ummar Namibia, daga cikinsu akwai shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta Kudu, wanda ya bayyana marigayin a matsayin babban jigo mai kishi jam’a da kuma ƙasarsa.
Marigayi Nujoma ya tashi a wani gida na masu ƙaramin ƙarfi, kuma ya fara aiki ne a da Hukumar Jiragen ƙasa a 1949, kafin a 1960 ya kasance jagoran ƙungiyar SWAPO wadda a ƙarƙashin inuwarta ce ya yi gwagwarmayar har zuwa samun ‘yancin kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI