Itopiya ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba ga Sudan

Itopiya ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba ga Sudan

Itopiya ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba ga Sudan wadda ta kwace mata yankin Fashka da ke kan iyakarsu.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Itopiya ta fitar ta ce, abun takaici ne yadda duk da Sudan na shugabantar Kungiyar Cigaban Kasashen Gabashin Afirka (IGAD) amma ta mamayi kasar Itopiya inda ta tilastawa fararen hula yin gudun hijira tare da zama jagorar kawo hatsarin rashin zaman lafiya a yankin.

Sanarwar ta kara da cewa, "Muna kira ga kasashen duniya da su matsa lamba ga Sudan kan ta janye dakarunta daga kasarta."


News Source:   ()