Jaridar New York Times dake Amurka ta bayyana cewa, gwamnatin Itopiya ta kori wakilinta a kasar Siman Marks.
Tsawon shekaru 2 Siman Marks na aiki a Itopiya kuma ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter bayan korar tasa zuwa kasar waje.
Marks ya bayyana cewa, ya shirya wani rahoto kan Kyautar Nobel ta Zaman lafiya da Firaminista Abiy Ahmed ya samu, kuma a ranar Alhamis din nan sai aka kore shi daga kasar.
Marks ya soki yadda ake gallazawa tare da cusgunawa 'yan jaridu a Itopiya.
Ya ce, "Ma'aikatan Hukumar Shige da Fice na Itopiya sun kore ni daga kasar kuma duk nema cikin ladabi da na yi na su ba ni izini na yi bankwana da dana mai shekaru 2 da karena amma suka ki."
Gwamnatin Itopiya ba ta ce komai ba game da korar dan jaridar daga kasar.
Marks ya rubuta wani labari dake ikirarin sojojin Itopiya da 'yan tawayen Eritiriya na hada kai wajen aikata kisan kare dangi a yankin Tigray.