Kamar dai yada kotu a Italia ta sanar mawakiyar Mali Rokia Traoré, wanda aka ba da sammacin kasa da kasa a shari'ar rashin wakilcin yaro, za a mika ta ga Belgium "a cikin kwanaki goma".
Da samun wannan labari, Jan Goossens, tsohon abokin mawakiyar,ya bayyana farin cikinsa,wanda lauyansa ya ruwaito cewa yana fatan cewa, da zarar mawakiyar ta zo, "zai iya samun ingantacciyar mafita don jin dadi da kuma rayuwa da 'yarsa.
A cikin 2019, kotun Belgium ta ba wa mahaifinta hakkin kula da 'yar mawakiyar, a Belgium, tare da hakkin ziyarta. Amma, daga baya, tsarin shari'a na Mali ya ba da damar tsare yar dake tsakanin su ga mahaifiyar kadai a Mali.
Tun daga wannan lokacin, an bayar da sammacin kama mawakiyar Mali Rokia Traoré, hakan ya kai kotun Belgium a bara yanke mata hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari saboda rashin wakilcin yaro.
A watan Yuni, an kama Rokia Traoré a Italia a wani lokaci da ta ke kokarin zuwa wani wurin holewa.
Yanzu kam mawakiyar ta daukaka kara kan hukuncin da kotun Brussels ta yanke, tare da bayyana cewa an tauye mata hakkinta tun lokacin da aka yanke mata hukunci ba tare da lauya ba yayin shari'ar 2023. Don haka ta sake samun kanta a gaban kotunan Belgium domin warware takaddamar da ke tsakaninta da mahaifin ’yarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI