Gwamnatin Italiya ta bukaci da a gudanar da bincike na gaskiya game da mutane da dama da aka gano an binne su a ramuka da dama a yankin Terhune na Libiya.
Gwamnatin ta Italiya ta fitar da sanarwar cewa "Yanayi ne mummuna kuma mai tayar da hankali, yadda aka samu ramuka da yawa da aka binne mutane da dama a cikinsu a yankin Terhune na Libiya."
Sanarwar ta ce "Italiya na kira da a gudanar da bincike na gaskiya don nemo wadanda suka aikata wannan danyen aiki. Itliya na kira ga dukkan bangarorin da ke rikici da juna da su girmama dokokin kasa da kasa na kare hakkokin dan adam."
A ranar 5 ga watan Yuni ne dakarun Libiya da suka kori mayakan Haftar daga garin Terhune suka gano gawarwakin mutane 106 a wani asibiti, a ranar 12 ga watan kuma suka gano wasu ramuka 3 da aka binne mutane da yawa a cikinsu.