A karkashin aiyukan yaki da annobar Corona (Covid-19), Indiya ta baiwa Najeriya kyautar alluran riga-gafi guda dubu dari.
Jakadan Indiya a Abuja, Abhay Thakur ya shaida cewa, an mika alluran riga-kafin da kasarsa ta aiko zuwa najeriya ga ofishin Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) da ke Abuja.
Thakur ya ce, wannan kyauta da Indiya ta baiwa Najeriya na nuni da irin karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen 2.
Najeriya ta karbi alluran riga-kafi miliyan 4 da dubu 224 na kamfanin AstraZeneca karkashin shirin COVAX na kasa da kasa da kuma kamfanin sadarwa na MTN.
A ranar 5 ga Maris aka fara yin allurar riga-kafin, kuma ya zuwa yanzu an yi wa sama da mutane dubu 700.