Wannan tallafin dai ya zo kan lokaci ga Nijar da ke samun bunkasuwar tattalin arziki amma har yanzu tana fuskantar kalubalen tsaro da na kudi.
Sanarwar da gwamnatin sojin kasar ta fitar ta ce, a cikin kudin za a yi amfani da aala miliyan 17 wajen daidaita tattalin arzikin Nijar, sai kuma dala miliyan 26 da aka ware domin magance matsalolin da suka shafi yanayi.
Wannan taimakon na zuwa ne a daidai lokacin da hasashen tattalin arzikin kasar Nijar ya samu ci gaba sosai, inda aka yi hasashen samun karuwar kashi 8.8 cikin 100 a shekarar 2024, wanda asusun IMF ya bayyana a matsayin babban ci gaba.
Sai dai IMF ya bayyana damuwarsa kan yadda ake gudanar da harkokin kasafin kudin Nijar, inda ya bukaci gwamnati da ta inganta ayyukanta na yaki da cin hanci da rashawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI