Tun a shekara ta 2022 ne kasar ta Nijar ta cimma wannan yarjejeniya da asusun Lamuni na duniya IMF inda a yanzu asusun ya damƙawa ƙasar waɗannan kudi.
Nijar na gabatar da wasu tsare-tsare, tare da IMF domin taimaka mata farfado daga mashassharar da ta fada na tattalin arziki, tun bayan bullar annobar Covid-19.
Rahoton da IMF ya fitar a 2022, ya yi kiyasin cewa kasar za ta farfado da tattalin arzikinta da kashi 7.1, amma idan ta fi mayar da hankali ga bangaren noma da kuma jan hankulan masu sanya hannayen jari.
Masana tattalin arziki na ganin cewa, idan har kasar ta yi amfani da matakan da suka dace, to kuwa za ta iya magance matsalolin tattalin arzikin da take fama da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI