![Ɗimbin mata na fuskantar cin zarafi ta hanyar fyaɗe a Sudan- HRW](https://iqra-media.s3.eu-west-2.amazonaws.com/public/AP24319608059434__ScaleWidthWzEwMDBd.jpg)
Cikin wani rahoto da human Rights Watch ta fitar a jiya Talata bayan wani bincike da ta gudanar ne ke bayyana hakan, rahoton da ke zuwa bayan yawaitar zarge-zarge game da cin zarafin da mata ke fuskanta a yaƙin ƙasar na kusan shekaru 2.
Sai dai duk da fitar wannan rahoto, RSF ta ƙi cewa komai dangane da wannan zargi na aikata ta’asa, ko da ya ke tun a baya ta sha musanta zarge zargen cin zarafi a yakin na sama da watanni 20 tsakaninta da Sojin Sudan, yaƙin da zuwa yanzu ya gama ragargaza ƙasar bayan raba mutane aƙalla miliyan 12 da muhallansu.
Kungiyar ta HRW mai shalkwata a birnin New York, ta ce ta tattara bayanai kan laifuka 79 na fyade akan mata manyansu da ƙananansu har ma da ‘yan ƙasa da shekaru bakwai.
Ƙungiyar ta ce ta yi hira da mutane bakwai da suka tsira, ciki har da wadda ta ce RSF na tsare da wasu mata 50, kuma ita ma an yi mata fyade akai-akai tsawon watanni uku.
Rahoton ya ce mayakan sun kai hari kan wasu mata 'yan kungiyar Nuba da ke wani yanki mai nisa da ke kan iyaka da Sudan ta Kudu, kuma hare-haren sun kai a yi tuhuma akai domin sun kai mataki na laifukan yaki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI