Ibtila'in fashewar dutse mai aman wuta a Kongo

Ibtila'in fashewar dutse mai aman wuta a Kongo

Mutane 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar dutsen Nyiragongo mai aman wuta dake gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa, sama da mutane dubu 25 sun yi hijira daga yankin sakamakon fashewar dutsen.

A daren ranar Asabar din karshen makon nan ne dutsen ya fara aman wuta bayan yin bindiga, kuma ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 15.

An bayyana cewa, sakamakon fashewar dutsen Nyiragongo dake daya daga cikin duwatsun Volcano a duniya, mutane dubu 5 sun yi hijira zuwa kasar Ruwanda makociyar Kongo.

Bayan fara aman wuta da dutsen ya yi, gwamnati ta fara kwashe jama'a daga yankin.

A shekarar 2000 dutsen Nyiragongo ya yi aman wuta tare da kashe mutane 250, wasu dubu 120 kuma suka bar matsugunansu.


News Source:   ()