Hungary za ta tura dakarunta 200 zuwa Chadi

Hungary za ta tura dakarunta 200 zuwa Chadi

Sanarwar na zuwa ne a yayin da shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby ke ziyara a Hungary a ƙarshen mako, inda ya gana da firaministan a birnin Budapest.

Mr. Orban ya bayyana Chadi a matsayin muhimmiyar ƙasar da ta shafe tsawon lokaci tana tsayin-daka wajen yaƙi da kwararar baƙin haure da kuma daƙile ayyukan ta'addanci.

Kodayake babu wani cikakken bayani game da manufar Orban ta tura dakaru har guda 200 zuwa Chadi.

Ba kasafai ake samun dakarun Hungary a ƙasashen Afrika ba, yayin da take ci gaba da haɓɓaka hulɗarta da Rasha da China.

Masana sun bayyana cewa, bisa dukkan alamu Hungary na neman ƙarkata aƙalarta zuwa Afrika kamar yadda China da Rasha ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)