Ƙungiyar ta kasa da kasa ta yi kira ga sojojin Rwanda da ƴan tawayen M23 da su bayar da tabbacin samun damar kai kayan agaji da isar da su ga jama'a, musamman ga mutanen da suka rasa matsugunansu.
Clémentine de Motjoye , shugabar sashen gudanar da bincike a yankin kasashen gabashin Afrika da ke aiki da ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce ƴan gudun hijira a Goma na cikin wani yanayi da ke tayar da hankali, kuma sama da ƴan gudun hijira miliyan 1 ne ke rayuwa a waɗannan wurare.
A gefe guda kuma, Rwanda ta yi maraba da taron da ƙungiyoyin Afrika 2 suka kira domin tattauna rikicin na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
a makon da ya gabata ne Shugabannin ƙasashe da ministocin ƙungiyar ƙasashen da ke kudancin Afrika suka gudanar da taro a babban birnin Zimababwe, kan rikicin Congo da a yanzu haka ke zama barazana ga tsaron yankin.
Sai dai shugaban Rwanda Paul Kagame bai halarci taron ba kasancewa ƙasarsa ba ta cikin ƙungiyar, amma shugaban Congo Felix Tshisekedi ya halarta ta kafar bidiyo.
A cewar ƙwararru na Majalisar Dinkin Duniya, ‘yan tawayen na samun goyon bayan dakarun Rwanda kusan 4,000, fiye da waɗanda suka taimaka musu a shekarar 2012 lokacin da suka ƙwace iko da Goma na ɗan gajeren lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI