Human Rights Watch ta damu matuka da ta'asar da sojojin Mali suka aikata kan fararen hula

Human Rights Watch ta damu matuka da ta'asar da sojojin Mali suka aikata kan fararen hula

 

A karshen shekarar 2023, tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali (Minusma), wanda ya hada da sojoji da 'yan sanda kusan 15,000, ya kawo karshen aikinsa bayan kusan shekaru goma na aiki wanzar da zaman lafiya.

Bisa kididdigar da kungiyar kare hakkin bil'adama ta yi, sojojin Mali da ke da alaka da sojojin haya na Wagner daga Rasha  sun "kashe da gangan" a kalla fararen hula 32 a tsakiya da arewacin kasar tun daga watan Mayun 2024.

Kungiyar Support Group for Islam and Muslim (GSIM), wata kungiyar masu jihadi dake da alaka da Al-Qaeda, da kuma kungiyar Islamic State in the Greater Sahara (EIGS), ne ke da alhakin mutuwar fararen hula akalla 47, tare da raba dubbai da muhallansu tun watan Yuni.

Kungiyar ta bukaci kara zurfafaf bincike don gaskanta wadanan alkaluma da ta ke da su.

"Tun bayan tafiyar rundunar wanzar da zaman lafiya ne Minusma shekarar da gabata , yana da matukar wahala a sami cikakken bayani game da cin zarafi, kuma kungiyar ta bayyana  damuwa matuka cewa lamarin ya fi yadda ake zato," in ji Ilaria Allegrozzi, mai bincike kan Sahel.

Rahoton na HRW ya dogara ne kan hirar da aka yi da shaidu 47, da majiya mai tushe, da kuma nazarin hotuna da hotunan tauraron dan adam da aka wallafa a shafukan sada zumunta da HRW ta tabbatar.

Kungiyar ta ce ta aike da sakamakonta ga gwamnati, ba tare da samun amsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)