Daidai lokacin da kiraye-kiraye ke ci gaba da yawaita bayan bikin ranar yaƙi da aiwatar da hukuncin kisa na duniya da ya gudana a jiya Alhamis, ƙungiyar Amnesty International ta ce ana ganin ƙaruwar yanke hukuncin kisa a ƙasashen yamma da saharar Afrika, duk da cewa nahiyar gabaki ɗaya ba ta yi shura wajen zartas da makamancin hukuncin ba in banda Somalia da ke kan gaba wajen aiwatarwa.
A cewar Amnesty International daga bara zuwa bana kaɗai anga ƙaruwar yanke hukuncin kisan daga mutum 298 zuwa mutum 494 a bana, wanda ke matsayin ƙaruwar kashi 66.
Amnesty International ta bayyana cewa ƙasashen Afrikan 10 su ne kan gaba wajen aiwatar da hukuncin kisan da inda adadin mutanen da Ghana ke zartaswa makamancin hukuncin ya ƙaru daga 7 a bara zuwa 10 a bana, sai Mali daga mutum 8 a bara zuwa 13 a bana kana Najeriya da jumullar mutum 246 daga mutum 77 a bara.
Amnesty International ta ce zuwa yanzu ƙasashen Afrika 24 cikin 53 sun dakatar da yanke hukuncin kisa a baya-bayan nan har da Gambia da Kenya da kuma Zimbabwe waɗanda yanzu haka ke tattaunawa kan yiwuwar dakatar da zartas da makamancin hukuncin.
Ko a shekarar da ta gabata ta 2023, Amnesty International ta sanar da ƙaruwar yankewa da kuma aiwatar da hukuncin na kisa a duniya baki ɗaya da jumullar mutum dubu 1 da 153 daga mutum 883 a 2022.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI