Hukumar Kula da Sadarwa ta kasar Mali (HAC) ta yanke shawarar rufe gidan talabijin na Joliba ta hanyar janye lasisin sa, kamar yadda wani jami'in tashar ya shaidawa AFP bisa sharadin sakaya sunansa.
Za a fara aiwatar da matakin daga ranar 26 ga Nuwamba, in ji majiyar.Matakin na zuwa ne bayan korafin da Majalisar Koli ta Sadarwa ta Burkina Faso ta yi a ranar 12 ga watan Nuwamba kan Labaran Talabijin na Joliba.
存档地图 / 非洲国家:马里和布基纳法索。 Carte Afrique / Mali et Burkina Faso © FMM Studio graphiqueWannan korafi ya biyo bayan ficewar Issa Kaou N'Djim, wani jigo a siyasar kasar Mali wanda ya shahara da goyon bayan shugaban mulkin sojan mulkin soja, Kanar Assimi Goïta, kafin ya nisanta kansa.
Issa Kaou N'Djim, a yayin watsa shirye-shirye a wannan gidan talabijin na cikin gida, "ya furta wasu kalamai mararsa dadi a kan hukumomin Ouagadougou" a kan sojojin da ke mulki a wannan makwabciyar kasa ta Mali. A cikin jawabin nasa, Issa Kaou N'Djim ya soki tsarin sojojin Burkina Faso a fanin da ya shafi tsaro da dai sauren su.
An sanya wa N'Djim sammacin kama shi a Bamako a ranar 13 ga Nuwamba saboda "laifi da ya aikata a kan wani shugaban kasa." A ranar 23 ga watan Disamba ne za a gurfanar da shi gaban kuliya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI