Hukumomin Mali sun fara fito na fito da masu hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba

Hukumomin Mali sun fara fito na fito da masu hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba

Daga cikin matakan da majalisar zastaswan Malin za ta dauka don takawa masu hakar ma’adinain ba bisa ka’ida ba birki ,sun hada da  na  gajeren zango da tsaka tsakiya da kuma na dogon lokaci.

A matakin farko tuni aka rusa wajen hakan ma’adinai ba bisa ka’ida ba guda 61 da na’urorin hakan ma’adinai 286 tare da motoci  63 wadanda ake amfani dasu wajen gurgunta tattalin arzikin kasa tare da da gurbata muhalli wanda ke barazana ga lafiyar al’umma, a cewar ministan ma’adinai Amadou Keita.

Ya kara da cewa dalilin wadannan mutane ana samun masu damfara da safarar mutane da kuma daukar nauyin ta’addanci wanda gwamnatin ba za ta lamunta ba duk da cewa wannan ba sabon al’amari bane

 Mali tana samar da Zinari ton 6 a shekara daga kananan masana’antu kuma ana bukatar bunkasa lamarin zuwa ton tsakanin 30 zuwa 57 a shekara, lamarin da aka ce tun cikin shekarar 2022  da 2023 ta yi kiyasin hakan ton 66

Majalisar Dinkin Duniya ta alakanta masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba fadace fadacen ta’addanci.

 

 

.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)