Hukumomin Mali sun cafke ma'aikatan kamfanin hakar ma'adinai na Canada guda hudu

Hukumomin Mali sun cafke ma'aikatan kamfanin hakar ma'adinai na Canada guda hudu

Mali na fama da rashin tsaro musaman a arewacin kasar inda masu da’awar jihadi dauke da makamai ke cin karnen su ba babbaka.

Gwamnatin mulkin sojan kasar ta sha alwashin tabbatar da cewa kasar Mali, daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen samar da zinari a nahiyar Afirka, amma kuma daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, ta samu daidaito wajen rarraba kudaden shiga na ma'adinai.

Wasu ƴan gudun hijirar Burkina Faso a ƙasar Mali Wasu ƴan gudun hijirar Burkina Faso a ƙasar Mali © UN

Da yake magana bisa sharadin sakaya sunansa, wata majiyar shari’a ta fada jiya Asabar cewa an kama wasu ma’aikatan Barrick Gold guda 4 yan kasar Canada a farkon makon, sai dai ba ta bayyana sunayensu ba, da kuma dalilin da yasa aka kama su.

 Wata majiya da ke kusa da kamfanin, wadda kuma ta nemi a sakaya sunanta, ta ce an bayar da belin manyan mutanen da ake tsare da su.

Zinare Zinare © GettyImages/Israel Sebastian

Barrick Gold yana da kashi 80 cikin 100, yayin da kasar Mali ke da sauran kashi 20 cikin 100, na kamfanoni biyu da suka mallaki rukunin zinare na karkashin kasa da na Loulo-Gounkoto a yammacin Mali, kusa da iyakarta da Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)