Hukumar zaben Tunisia ta fitar da sunayen yan takara uku a zaben kasar

Hukumar zaben Tunisia ta fitar da sunayen yan takara uku a zaben kasar

Daga cikin yan takara da suka samu amincewar hukumar Isie karkashin Shugabancin Farouk Bouasker,wanda yayin wani taron manema labarai ya tabbatar da cewa an kawar da sauran yan takara 14 "bayan nazarin takardunsu kuma saboda "ba su tattara isassun kudade ba.

Wakilan hukumar zaben Tunisia Wakilan hukumar zaben Tunisia REUTERS/Zoubeir Souissi

Baya ga shugaban kasar da ke neman wa'adi na biyu, sauran 'yan takara biyun sun hada da Zouhair Maghzaoui, tsohon mataimakin mai kare ra'ayin larabawa, da kuma Ayachi Zammel, wanda shi ma tsohon mataimakin shugaban wata karamar jam'iyya ce.

Ma'akatan hukumar zaben Tunisia Ma'akatan hukumar zaben Tunisia AFP - YACINE MAHJOUB

Ana kalon shugaban kasar kuma dan takara a wannan zabe a matsayin wandake gudanar da mulkin kama karya bayan zaben sa a shekarar 2019,sai dai  daga lokacin ‘yan adawa da kungiyoyin kare hakokin Bil Adam ke zarginsa da karkatar da mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)