Hukumar lafiya ta Duniya na nazarin inganta rigakafi don rage yaduwar cutar kyandar biri

Hukumar lafiya ta Duniya na nazarin inganta rigakafi don rage yaduwar cutar kyandar biri

Hukumar ta WHO ta fada a cikin wata sanarwa ga manema labarai cewa taron da zai gudana ranar Laraba zai kasance  mai muhimanci ganin shawarwari da kwarraru za su dau  a wannan karo.

Kyandar biri a DRCongo. Kyandar biri a DRCongo. © wikimedia commons

 Shugaban hukumar lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya rubuta a shafinsa na X ya na mai cewa  "Kwamitin zai gabatar masa da shawarwari da ya dace a yi amfani da su biyo bayan barkewar wannan cuta,har idan ta kama a sake dabaru ta bangaren kariya,hukumar za ta duba yiyuwar hakan.

Cutar ta kyandar biri da aka fi sani da Monkeypox, cuta ce mai saurin yaduwa ta hanyar kwayar cuta da dabbobi ke yadawa ga mutane amma kuma ana kamuwa da ita daga mutum zuwa mutum ta hanyar kusancin jiki.

Kwayoyin cutar kyandar biri Kwayoyin cutar kyandar biri © NIAID/NIH

Cutar na haifar da zazzaɓi, ciwon tsoka da manyan raunuka irin na fata. Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ita ce kasar da a halin yanzu ta fi fama da cutar, inda aka tabbatar da mutane 14,479 da ake kyautata zaton sun kamu da cutar a ranar 3 ga watan Agusta da kuma mutuwar mutane 455, a cewar hukumar lafiya ta Tarayyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)