Cutar wadda ta faro daga jamhuriyar dimokradiyyar Congo ta tsallaka zuwa maƙwaftan ƙasashe lamarin da ya yi ajalin ƙananan yara da dama.
Da yake jawabi shugaban hukumar ta CDC Jean Kaseya ya ce abin takaici ne yadda cutar ta rika yaduwa cikin hanzari, duk kuwa da matakan da ake ɗauka na shawo kanta amma lamarin ya ci tura.
Kawo yanzu dubban mutane sun kamu da cutar musamman a yankin gabashin Afrika yankin da ke da ƙasashe masu fama da matsalolin rashin zaman lafiya da kuma tsananin talauci.
Zuwa yanzu cutar ta kama mutane sama da dubu 15 cikin su kuma 461 sun rasa rayukansu, abinda ke nufin cutar ta kai kaso 160 idan aka kwantanta da adadin da aka gani a bara, da bai kai haka ba.
Hukumar ta ce wannan ba wai sanarwa bace kawai, kira ne ga mahukunta da kuma jama’a da su kara kaimi wajen daukar matakan dakatar da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI