Hukumar kwallon kafar Libiya(LFF) ta daukaka kara kan hukuncin da CAF ta yanke akanta a dambarwar su da tawagar Super Eagles ta Nijeriya a wasan nema gurbin shiga gasar cin kofin Afirka AFCON da za’a yi a kasar Maroco a shekara 2025.
Jarida Alwasat-Ly mai sharhi gameda harakokin wasani a Libiya, ta ce LFF na kallon hukuncin CAF amatsayin rashin adalci a gareta ganin yadda ya mayer da ita mataki na karshe a rukunin su da D.
Wannan dai ya biyo bayan ƙorafin da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta shigar, kan yadda ta zargi hukumomin Libya da yin watsi da su a lokacin da suka je ƙasar don buga wasa na biyu na neman gurbin shiga gasar lashe kofin Afrika AFCON na shekara mai zuwa.
Hukumar Kwallon Ƙafar Libya ta ce ba wai da gangan ba ne abun ya faru, sannan kuma ta ce itama irin haka ta faru da ƴan wasanta a lokacin da suka je Najeriya don buga wasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI