HRW ta zargi Chadi da kisan ɗimbim masu zanga-zanga da ta tsare a 2022

HRW ta zargi Chadi da kisan ɗimbim masu zanga-zanga da ta tsare a 2022

Akalla fursuna 4 ne suka mutu a kan hanyar su ta zuwa gidan yarin Koro Toro, inda wasun  6 na daban suka rasa rai, kana ta yiwu wani mutun  guda shima ya mutu, inji rahoton  HRW.

 Yayin zanga zangar nuna adawa da shirin  tazarcen Shugaban gwamnatin rikon kwarya  kasar,  Mahamat Deby Itno  na  shekaru biyu kan kujera mulki ne, jami’an tsaron kasar suka bude wuta kan masu zanga zanga inda suka hallaka mutun 60.

Kazalika, an tsare wasu daruruwan mutane wadanda daga bisani aka kai su gidan kason Koro Toro mai nisan kilomita 600 daga N’djamena baban birnin kasar.

A wancen lokacin, kungiyar Human Rights Watch  ta bukaci mahukuntan kasar Tchadi, da tarayya Afirka da ma kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da su gudanar da bincike mai zaman kansa kan abunda ta kira tsare jama’a ba bisa ka’ida ba, cin zarafi da kuma kisa a gidan yarin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)