Carine Kaneza mataimakiyar shugabar ofishin kungiyar kare hakkin bil'ada ta Human Rights Watch mai kula da nahiyar Afirka, ta bayyana cewa wannan mataki ne da ke matsayin babbar barazana, domin kuwa daga cikin wadanda aka kama aka tura fagen daga, akwai ‘yan jarida, da masu sukar lamirin gwamnati, da ‘yan adawa da kuma sauran masu fafutuka karkashin inuwar kungiyoyin fararen hula.
Mafi yawansu an tarar da su a cikin gidajensu ne aka yi awun gaba da su, wasu kuwa a wuraren ayyukansu, saboda za mu kira wannan a matsayin wuce gona da iri. Wannan wata siyasa ce aka bullo da ita domin tursasawa da kuma cin zarafin jama’a.
Idan ka dauki misalin alkalan da aka tilasta wa zuwa fagen daga, dukkaninsu suna aikin bincike ne a kan muhimman batutuwa da suka shafi abubuwa na assha da gwamnatin mulkin sojin kasar ta aikata.
Bayan sun afka wa masu ‘yan adawa, da masu fafutuka, a yau sojojin sun akfa wa bangaren shari’a ne, kuma gaskiya wannan abu ne da bai dace ba..
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI