
A ranar 7 ga watan Fabrairu ne mayaƙan IS suka kai hari kan wani ayarin motoci ɗauke da fararen hula sama da 100, akasarin su masu haƙar zinare daga Nijar, da ‘yan kasuwa daga Mali, a cewar rahoton Human Righs Watch.
Ƙungiyar kare hakkin ɗan adam din ta ce kamata ya yi mahukuntan Mali su nemi wata hanyar bai wa fararen hula kariya ta wajen hada su da jam’ian ƴan sanda waɗanda ba su ne ƴan ta’addan ke nema ba.
Mali, kasar da ke yankin Sahel, wadda ke ƙarƙashin mulkin soji tun bayan juyin mulki biyu a shekarar 2020 da 2021 tana fama da matsalar tsaro sakamakon ayyukan ƴan ta’adda masu alaƙa da al-Qaeda da kuma ƴan tawaye masu neman yancin Abzinawa.
Tun bayan da sojoji suka ƙwace ragamar mulki ne ƙasar ta kawo ƙarshen ƙawance ta fannin tsaro da tsohuwar uwargijiyarta, ta kuma koma wa Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI